12 Yuli 2021 - 12:20
Shugabannin Kamaru Da Na Mali, Sun Taya Zababben Shugaban Iran Murna

Shugabannin kasashen Jamhuriyar Kamaru da kuma na Mali, sun taya zababben shugaban Iran Ebrahim Ra’isi, murna kan nasarar da ya samu a zaben shugabacin kasar ta Iran.

ABNA24 : ya fitar, ranar Juma’a, ofishin jakadancin Iran a Najeriya, ya ce ya samu sakon taya murna daga shugaba Paul Biya na Jamhuriyar Kamaru.

Sakon ya kuma jadadda bukatar karfafa alaka a tsakanin kasashen biyu.

A wani labarin kuma da ofishin jakadancin Iran, a Bamako, ya fitar, shugaban kasar Mali, Assimi Goïta, ya aike da sakon taya murna ga zababben shugaban kasar ta Iran, tare da yi masa fatan alkhairi.

A sakon nasa Shugaban Malin, ya bayyana cewa a shirye ya ke don karfafa alaka da Jamhuriyar musulinci ta Iran domin samar da ci gaba mai daurewa.

342/